An yi satar shiga Old Trafford

Wasu magoya bayan Man United biyu da suka
boye a bandakin Old Trafford suka kwana a
daren Juma'a domin su kalli wasan kungiyar da
Arsenal kyauta sun fitar da bidiyon yadda suka
tsara abin.
Magoya bayan suna cikin tawagar da ta je
ziyarar bude ido a filin wasan ne, amma suka
sulale daga cikin abokan ziyarar tasu, suka buya,
domin kallon wasan.
A ranar Asabar da safe ne aka gano su, a lokacin
da ake bincike filin wasan, domin shirye-shiryen
wasan.
Daya daga cikin matasan biyu mai suna Uosof
Ahmadi ya gaya wa BBC cewa su kam sun yi
tsammanin komai zai tafi daidai saboda irin
dabarar da suka yi suka tsara abin.
Matashin dan shekara 21, ya ce, shirin na
kwanan zaune na sa'a 24, abu ne da ake yi a
YouTUbe, kuma yadda ya shafe dare a shagon
M&M World da gidan abinci na McDonald, ya
sanya hoton bidiyonsa na yadda ya yi kokarin
gwada irin wannan abu a filin wasan Arsenal a
farkon watan nan.
Bayan da masu kula da filin sun kama Uosof
Ahmadi da abokinsa Kyle Morgan-Williams sun
mika su ga 'yan sanda, wadanda su kuma suka
sallame su ba tuhuma.
Lamarin ya faru ne watanni shida bayan da
kwatsam aka dage wasan Premier na Man
United da Bournemouth a filin, lokacin da aka
gano kunshin wani abu a filin.
Daga baya an gano cewa wani abin fashewa ne
na bogi da ka bari a filin bayan atisayen 'yan
wasa a makon.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An yi satar shiga Old Trafford"

Post a Comment