An gano birnin da ya shekara 5,000 a Masar

Masu binciken kayan tarihi na karkashin kasa a
Masar sun gano wani birni wanda ya fi shekara
5,000 da wasu gine-gine, ciki har da gidaje da
tukwane da manyan kaburbura.
An gano birnin ne a lardin Sohag da ke kudancin
kasar ta Masar, yankin da birnin Luxor, daya
daga cikin wuraren da masu ziyarar bude ido
suka fi zuwa, yake.
Masana sun ce girman kaburra 15 da aka gano
ya nuna cewa mutanen da aka binne a cikinsu
masu-fada-a-ji ne na wancan zamanin.
An yi amannar cewa mutanen da suka zauna a
birnin manyan jami'ai ne da kuma magina
kaburbura, wadanda watakila suka gina kaburran
manyan sarakuna a birnin Abydos - inda aka gina
wuraren bauta da dama, kuma babban birni na
farkon tarihin daular Masar ta wancan lokacin.
Farfesa Chris Eyre, masanin tarihin kasar Masar
da ke Jami'ar Liverpool, ya shaida wa BBC
cewa: "Akwai wata babbar makabartar da ake
binne sarakunan waccan daular kusan mil daya
daga wurin da aka gano wannan birni. Hasalima
mun fara samun sunayen sarakunan da aka
binne a makabartar. Don haka ina ganin wannan
gari shi ne birnin farko a tarihin Masar."
An gano wanna birni ne a lokacin da hukumomin
kasar ke kokarin farfado da fannin bude ido na
kasar, wanda ya fuskanci koma-baya sakamakon
hatsaniyar siyasar da aka rika yi a shekarun baya
bayan nan.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An gano birnin da ya shekara 5,000 a Masar"

Post a Comment