Trump zai biya daliban jami'arsa miliyoyin daloli

Zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump
ya yi amai ya lashe bayan da ya amince cewa
zai biya miliyoyin daloli akan wata badakalar
shari'a data mamaye yakin neman zaben sa.
Wasu tsofaffin dalibai ne dai suka gurfanar da
shi a gaban kotu akan kaddarorin jami'ar sa wato
Trump University.
A baya dai yayi ta nanata cewa shi ba zai biya
komai ba amma a yanzu ya amince ya biya dala
miliyan 25.
Mai shigar da kara a birnin New York ya bayyana
matakin da cewa tamkar yin amai ne a lashe sai
dai lauyan Mr Trump ya ce wannan ya nuna
aniyarsa ta aje son kai gefe guda don tunkarar
kalubalen da kasar ke fuskanta.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Trump zai biya daliban jami'arsa miliyoyin daloli"

Post a Comment