Jirgin sama ya yi hadari da 'yan kwallon Brazil


Wani jirgin sama dauke da mutum 81, ciki har
da kulob din kwallon kafa na Brazil, ya fadi a
kusa da birnin Medellin na kasar Colombia.
Rahotanni sun ce akalla mutum shida ne suka
tsira. Jirgin ya samu matsalar na'ura ne.
Jami'an filin saukar jiragen sama sun ce jirgin,
wanda aka dauki hayarsa, ya taso ne daga
Bolivia yana dauke tawagar 'yan kwallon kulob
din Chapecoense.
Tawagar na shirin karawa ne a wasan karshe na
Copa Sudamericana tare da kungiyar Atletico
Nacional na birnin Medellin.
An tsara za a yi kashi na biyu na wasan karshe
na gasar wacce ita ce ta biyu a muhimmanci a
Kudancin Amurka a ranar Laraba, amma yanzu
an dage ta.
Hukumar kula da kwallon kafa ta Kudancin
Amurka (Conmebol) ta ce ta dakatar da dukkan
"aikace-aikacenta".

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jirgin sama ya yi hadari da 'yan kwallon Brazil"

Post a Comment