Obasanjo na yi wa Buhari zagon-kasa - 'Yan majalisa

'Yan majalisar wakilan Najeriya sun ce tsohon
Shugaban kasar Olusegun Obasanjo na yi wa
gwamnatin Buhari zagon-kasa, bayan da ya
zarge su cin hanci da rashawa.
Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta bayyana
Obasanjo a matsayin "mutumin da ya fi kowa cin
hanci a tarihin kasar".
Mai magana da yawun majalisar Hon Abdulrazak
Namdas ya ce "Abin takaici ne ya fara nuna
halayyarsa ta kawar da gwamnati da aka sanshi
da ita tun shekara 1979".
Ya kara da cewa "Ya yi hakan ga tsofaffin
Shagabanni da suka hada da Shehu Shagari,
Janar Buhari, Janar Babangida, da kuma Janar
Abacha kafin ya daure shi a kurkuku".
Olusegun Obasanjo, ya furta wadansu kalamai a
ranar Laraba a Lagos, inda ya soki gwamnatin
Buhari saboda yadda take yi wa gwamnatoci
ukun da suka gabata, ciki har da ta sa, kudin
goro wajen zargin rashin iya jagoranci.
Ya kuma bai wa Buhari shawara da ya daina
korafi kan abin da ya wuce, inda ya ce tun da an
zabe shi ne domin ya gyara Nigeria, ya kamata
ya mayar da hankali kan gyara barnar da ya
tarar.
Sannan ya nemi ya taka wa 'yan majalisun kasar
birki, yana mai cewa majalisar ce dandalin cin
hanci da satar kudin al'umma.
Sai dai Namdas ya ce a lokacin Obasanjo ne aka
baje kudi a majalissar tarayya domin bayar da
cin hanci, saboda a sauke Kakakin Majalisar na
wancan lokaci Ghali Umar Na Abba.
Ya kuma tambayi 'yan Nigeria cewar "Shin har
kun manta lokacin da Obasanjo ya yi amfani da
karfin ikonsa, inda ya dunga karbar kudade daga
wajen 'yan kasuwa da 'yan kwangila domin gina
katafaren dakin karatunsa?
Ya kuma ce Obasanjo ya taimakawa Buhari a
lokacin yakin zabe, amma tun lokacin da ya
fahimci cewar gwamnati mai ci tana fama da
tattalin arziki, sai ya juya da nufin yi mata zagon
kasa.
Kawo yanzu Mista Obasanjo bai ce komai game
da kalaman na 'yan majalisar ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Obasanjo na yi wa Buhari zagon-kasa - 'Yan majalisa"

Post a Comment