Fiye da mutane 70 sun hallaka a Mozambique

Hukumomi a kasar Mozambique sun ce fiye da
mutane 70 ne suka mutu yayin da 110 suka
samu munanan raunuka bayan da wata babbar
motar dakon man fetur ta fashe ta kuma kama
da wuta.
Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ce
mutanen da lamarin ya rutsa da su suna kokarin
kwasar man fetur ne bayan da babbar motar
dauke da man fetur ta fadi ta kama da wuta
saboda tsananin zafi.
Lamarin dai ya faru ne a lardin Tete dake kusa
kan iyakar kasar da Malawi.
Tuni gwamnati ta turo jami'ai zuwa yankin domin
tantance lamarin da kuma irin taimakon da
mutanen ke bukata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Fiye da mutane 70 sun hallaka a Mozambique"

Post a Comment