Mai gyaran takalmin da 'ya fi masu albashi samun kudi'

Idris, mai shekara 21, na daya daga cikin dimbin
matasa masu sana'ar gyara da wanke takalma, a
Najeriya.
Idris wanda dan asalin garin Isa ne da ke jihar
Sokoto, yana bi kwararo-kwararo a garin Kuje da
ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja, domin neman
aikin takalmi.
Ya kan fito bakin fama da zarar ya karya kumallo
kuma ba ya komawa makwancinsa har sai
la'asar sakaliya.
Mafi yawancin lokuta ma, Idris yana komawa
gida ne gefin almuru.
Dauke da akwatu tare da akwakun da ke kunshe
da kayan aikinsa, matashin yana karkada alharga
tare da marikin akwatun wadanda haduwarsu ke
bayar da sauti mai jan hankali ga
kwastomominsa da ke cikin gidaje har ma da na
waje.
Idris ya fada min cewa duk da cewa mutane
suna ta faman tsitsitsi da kukan rashin kudi
sakamakon halin karayar tattalin arzikin da
Najeriya ta samu kanta a ciki, har yanzu, ludayin
masu sana'a irin tasa, na kan dawo.
"A kullum ta Allah na kan yi aikin Naira 3000,
idan kuma ranar ba ta yi kyau ba, na kan iya
komawa gida da N1500." In ji Idris.
Ya kuma kara shaida min cewa yana zuba
adashin Naira Dubu a kowane wayewar garin
Allah.
Sannan kuma ya ci abinci da biyan bukatun yau
da kullum da ragowar kudin har ma ya
taimakawa mahaifansa.
"Da wannan sana'ar nake taimakawa iyayena da
'yan uwana."
Da na tambayi matashin ko ya yi karatun Boko
domin samun shaidar da za ta ba shi damar yin
aikin gwamnati domin samun albashi mai tsoka,
sai ya kada baki y ace min "ban yi karatun boko
ba kuma ba na yin da-na-sani."
"Sannan kuma ai nafi wasu ma'aikatan samun
kudi a karshen wata tunda an ce wasu
albashinsu bai wuce Naira dubu 39 ba."
To shin ko a nawa Idris yake wanke da gyara
takalma?
"Idan na sanya wa takalmi neuteral, Naira 50 ne,
idan kuma wanda ba neuteral ba ne, ina karbar
Naira 30."
Baya ga wanke da goge takalmi, sana'a irin ta su
Idris ta kunshi dinke takalman da sanya musu
gam idan sun daga.
Har wa yau, Idris yana dinke jakunkuna har ma
da gyaran tankunan ruwa na roba idan suna
zubar da ruwan.
Dangane kuma da burinsa a rayuwa, na tambayi
Idris, abin da yake son ya zama.
" Babban burina shi ne na zama mai kamfanin
yin takalma da kowa zai san da zamana."
To babu dai abin da zai gagari ubangiji, amma a
yanzu dai Idris na daya daga cikin daruruwan
masu gyaran takalmi a kasar da ake yi wa kallon
sana'arsu ba ta kai ga cire su daga marasa aikin
yi ba.
Ko Idris zai mallaki katafaren kamfanin yin
takalmin da yake mafarki, a nan gaba? Allah ne
kadai masani. To amma dai da alama ya fi wasu
masu daukar albashin da suke yi wa masu
sana'a irin tasa kallon sai-da-kaji sai-da-kaji.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mai gyaran takalmin da 'ya fi masu albashi samun kudi'"

Post a Comment