Nigeria: An bayar da belin mai shari'a Ngwuta kan miliyan 100

Wata babbar kotu a Nigeria ta bayar da belin
wani alkalin kotun kolin kasar bayan da ya
musanta aikata laifuka 15 da suka hada da
halatta kudaden haram da cin hanci.
An bayar da belin Sylvester Ngwuta a kan kudi
naira miliyan 100 da kuma kimar da yake da ita.
A zaman kotun na ranar Litinin, lauyoyinsa da na
gwamnati sun kai ruwa-rana kan batun belinsa,
amma daga bisani alkalin kotun ya amince da
bukatar ta sa.
Najeriya ta dauko hayar wani mai gabatar da
kara ne dan kasar waje domin ya jagoranci
rukunin lauyoyinta.
Mai shari'a Ngwuta na cikin alkalai bakwai
wadanda jami'an tsaro suka kai sumame
gidajensu a wani yunkuri na kawar da cin hanci
daga bangaren shari'a.
Kungiyar lauyoyi ta kasar ta yi Allah-wadai da
matakin da jami'an tsaron suka dauka.
Jami'an tsaron farin kaya na DSS sun kare
matakin na su, suna masu cewa "makudan
kudaden da suka samu ciki har da na kasashen
waje sun nuna yadda alkalan ke aikata ba daidai
ba".
Tuni dai hukumar NJC da ke sa ido kan fannin
shari'a a kasar ta dakatar da alkalan, wanda suka
musanta zargin da ake yi musu.
Wannan ne karon farko da aka gurfanar da wani
daga cikin alkalan.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin
yaki da cin hanci da rashawa wanda ya yi kasar
katutu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: An bayar da belin mai shari'a Ngwuta kan miliyan 100"

Post a Comment