An sace tsohon ministan Najeriya, Amb Bagudu Hirse

Rundunar 'yan sandar jihar Kaduna da ke
arewacin Najeriya ta tabbatar wa da BBC cewa,
an sace tsohon ministan harkokin waje na
kasar, Ambasada Bagudu Hirse, a ranar Lahadi.
Kakakin rundunar, ASP Aliyu Usman ya ce an
tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen jihar
domin gano inda aka kai tsohon ministan.
Jihar ta Kaduna ta yi kaurin suna wajen satar
mutane, inda ko a watan Yulin da ya gabata ma
aka sace jami'in jakadancin Saliyo, Manjo Janar
Nelson Williams ko da yake an sake shi bayan
kwashe kwanaki a hannun wadanda suka sace
shi.
Za mu kawo muku cikkaken bayani a nan gaba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An sace tsohon ministan Najeriya, Amb Bagudu Hirse"

Post a Comment