OPEC ta amince ta rage yawan man da take hakowa

Kasashen da ke kungiyar OPEC, masu arzikin
man fetur, sun amince su rage yawan man da
suke hakowa, a karon farko cikin shekara
takwas.
Muhammad Barkindo, babban sakataren
kungiyar, ya shaida wa BBC cewa za a fara rage
man da ya kai ganga miliyan daya da dubu dari
biyu daga watan Janairu.
Wannan na zuwa ne bayan sama da shekara ana
fama da faduwar farashin, wanda ya ragu da fiye
da rabi tun 2014, saboda yawaitarsa a kasuwa.
Farashin mai samfurin Brent ya tashi da kashi
9% zuwa sama da dala 52, yayin da man Amurka
kuma ya tashi zuwa dala 50.
Su ma kasashen da ba sa cikin kungiyar ta Opec
ana sa ran za su rage adadin da suke hakowa da
ganga 600,000 a kowacce rana.
Kasashen Najeriya, Iran da kuma Libya ba za su
rage na su adadin man ba saboda wasu
matsaloli da suke fama da su.
A watan Satumba ne kungiyar, mai mambobi 14,
ta amince ta rage yawan man da take samarwa.
Wannan yarjejeniya ta zo bayan wani taro da su
ka yi a Vienna, a kasar Austria, inda bambancin
siyasa tsakanin Iran da Saudiyya ya nemi kawo
cikas a lamarin.
Hakan dai labari ne mai dadin ji ga kasashe
kamar su Najeriya wadanda tattalin arzikinsu
yake tangal-tangal saboda faduwar farashin man.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "OPEC ta amince ta rage yawan man da take hakowa"

Post a Comment