An sace mutum fiye da 40 a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewacin
Nigeria sun ce 'yan bindiga masu fashin shanu
sun sace mutane fiye da arba'in a jihar.
A ranar Juma'a ne da dai masu fashin shanun
suka sace mutanen a lokaci guda domin yin
garkuwa da su.
Akasarin mutanen da suka yi awon gaba dasu dai
'yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta zuwa cin
kasuwa daga kauyukansu.
Rahotannin sun kara cewa 'yansanda biyu da
fararen hulla hudu sun rasa rayukansu a cikin
lamarin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An sace mutum fiye da 40 a Zamfara"

Post a Comment