Zakarun Turai: Kudin da Man United ke samu ya ragu

Kudin da Manchester United take samu ya ragu
sakamakon kasa samun cancantar shiga gasar
cin kofin Zakarun Turai ta Uefa, ta bana da ta
yi.
Kudin da kungiyar take samu a cikin watanni uku
na farkon shekara zuwa 30 ga watan Satumba ya
ragu da fam miliyan 3.4, (kashi 2.8 cikin 100).
Haka kuma kudin da take samu a ranar da take
yin wasa ya ragu da kashi 32.3 cikin 100, inda
kenan take samun fam miliyan 16.8. Ribar da
take samu ta zama fam miliyan 6.2.
Abin da ya fi haddasa raguwar kudin da kungiyar
ke samun shi ne, kasancewar wasannin da take
yi a gida sun ragu da guda uku, idan aka
kwatanta da wasannin da ta yi a daidai wannan
lokaci a 2015.
Bashin da ake bin ta kuma ya karu ne da kashi
18 cikin dari zuwa fam miliyan 337.7, sakamakon
faduwar darajar kudin Ingila, fam a kan dala tun
lokacin da aka kada kuri'ar ficewar Burtaniya
daga kungiyar Tarayyar Turai.
Babban darektan kungiyar ta Man United Ed
Woodward, ya ce, '' Yanayin kudin da muke ciki a
wannan lokaci ya nuna tasirin rashin shigarmu
gasar cin kofin Zakarun Turai ta Uefa.''
Sai dai kuma kudaden da kungiyar take samu na
tallace-tallace ya karu da kashi 4.4 cikin dari
zuwa fan miliyan 74.3, inda ake sa ran kudin da
take samu gaba daya a shekara ya kai tsakanin
fam miliyan 530 da miliyan 540.
Kungiyar ta sayi 'yan wasa hudu a lokacin
kasuwar sayen 'yan wasa da ta wuce, wadanda
suka hada da dan wasan tsakiya na Faransa,
Paul Pogba, wanda ya kasance mafi tsada a
duniya kan fam miliyan 89 da kuma dan Sweden
Zlatan Ibrahimovic.
Man United din yanzu ita ce ta uku a tebur din
Premier, sannan ta kai wasan dab da na kusa da
karshe na cin kofin kalubale na Lig (EFL Cup) na
Ingila, amma kuma tana cikin hadarin kasa kaiwa
zagayen sili daya kwale na gasar cin kofin
Zakarun Turai na Europa, yayin da ya rage
wasanni biyu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zakarun Turai: Kudin da Man United ke samu ya ragu"

Post a Comment