Nigeria: 'Talauci' ya hana bai wa tsoffin shugabanni albashi

Gwamnatin Najeriya ta ce matsin tattalin arziki
ya sa ta shafe wata 10 ba ta biya tsofaffin
shugabannin kasar alawus dinsu ba.
Sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal,
wanda ya bayyana hakan lokacin da wasu 'yan
majalisar dattawa suka kai masa ziyara a Abuja,
ya kara da cewa ba a bai wa tsofaffin
shugabannin kasar alawus dinsu ba ne saboda
babu kudin da za a biya su.
Ya kara da cewa tsofaffin shugabanni irin su
Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo da Shehu
Shagari suna bin gwamnati alawus tun watan
Janairu.
A cewarsa, "Akwai sashen da ke kula da biyan
alawun sin tsofaffin shugabannin kasar, amma a
halin da ake ciki babu kudi a sashen.
Muna sane da boren da wasu 'yan jihar Bayelsa
ke yi cewa ba a bai wa tsohon shugaba
Jonathan alawus dinsa ba, sai dai mun yi musu
bayani cewa ba shi kadai ba ne ke fama da
wannan matsala."
Najeriya dai ta fada matsanancin rashin kudi
sakamakon faduwa farashin mai da kuma zargin
da ake yi wa gwamnatocin da suka gabata na
sace kudaden.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: 'Talauci' ya hana bai wa tsoffin shugabanni albashi"

Post a Comment