Giyar gargajiya ta kashe mutum 21 a Kamaru

Wasu mutane 21 sun mutu a Kamaru bayan da
suka sha wata giyar gargajiya mai karfin tsiya, a
wani yanki na kasar Kamaru.
An kuma garzaya da wasu mutanen 22 da su ma
suka kwankwadi barasar wadda ake kira Odontol,
kamar yadda kafafen watsa labarai na
gwamnatin Kamarun suka sanar.
A yanzu dai hukumomi a garin Abong-Bang, na
Kudancin Kamaru, inda lamarin ya faru, sun
haramta yin giyar.
Ana yin giyar ne da ruwan bishiyar kwakwa, wato
bammi da sukari da kuma bawon wata bishiya da
ake kira essok a yankin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Giyar gargajiya ta kashe mutum 21 a Kamaru"

Post a Comment