Kusan mutum 100 sun mutu a hadarin jirgin kasa a India

'Yan sanda sun ce akalla mutum 96 ne suka
mutu yayin da fiye da mutum 100 suka jikkata a
wani hadarin jirgin kasa da ya abku a arewacin
India.
Jirgin da ke zirga-zirga tsakanin manyan birane
ya taso ne daga birnin Indore da ke tsakiyar
kasar zuwa birnin Patna da ke gabashin kasar
lokacin da ya kauce daga layin dogo kusa da
garin Kanpur.
Masu bayar da agaji sun yi ta kustawa cikin
taragwan jirgin suna cire mutane.
Har yanzu ba a san abin da ya yi sanadin
hatsarin jirgin ba.
Daya daga cikin fasinjojin jirgin, Krishna Keshav,
ta shaida wa BBC cewa: "Mun farka daga bacci
a firgice da kimanin karfe uku na dare. Taragwai
da dama na jirgin sun kauce daga layin dogo
lamarin da ya jefa kowa cikin dimuwa. Na ga
gawarwakin mutane da dama da kuma mutanen
da suka jikkata."
Ministan zirga-zirgar jiragen kasa na India ya
bayar da umurnin a gudanar da bincike a kan
hadarin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kusan mutum 100 sun mutu a hadarin jirgin kasa a India"

Post a Comment