Jiragen ruwan Netherland uku sun nitse a tekun Java na kasar Indonesia

Gwamnatin Birtaniya ta ce ta damu da wani
rahoto da ke cewa wasu jiragen ruwa da suka
nitse a lokacin yakin duniya na biyu, sun bace
ne daga kasan tekun Java.
Netherland ta tabbatar da cewa jiragen ta uku da
suka nitse wanda ta kira da kaburburan
mutanensu na bangaren mazan jiya, sun bace ne
tun daga wajen da ke gabar tekun Java a
Indonesiya.
Ana tunanin cewa an yi dai-dai da jiragen ne
domin amfani da karafunansu.
Ma'aikatar tsaron Jamus ta ce lalata kaburburan
sojojin da suka mutu a fagen daga, babban laifi
ne.
Sojojin ruwan Indonesiya sun ce za su yi bincike
akan wannan batu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Jiragen ruwan Netherland uku sun nitse a tekun Java na kasar Indonesia"

Post a Comment