Nigeria ta kulla yarjejeniyar gina hanyar kankare da Dangote

Gwamnatin Najeriya ta kulla yarjejenniya da
kamfanin Dangote domin gina hanyar kankare
mai nisan kilomita 42 daga garin Obajana zuwa
Kabba a jihar Kogi.
A yammacin ranar Talata ne bangarorin biyu
suka sanya hannu kan kwangilar a Abuja.
Babban sakatare a ma'aikatar ayyuka da gidaje
da wutar lantarki Injiniya Magaji Abdullahi Gusau
ne ya rattaba hannu a madadin gwamnatin
tarayyar.
Yayin da mai bai wa shugaban kamfanin na
Dangote shawara Injiniya Joseph Makoju ya sa
hannu a madadin kamfanin, yana mai cewa
"babban cigaba ne a tarihin Najeriya".
Kamfanin na Dangote zai kashe kimanin Naira
biliyan 11 da rabi a aikin, amma an ba shi aikin
ne a madadin biyan kudin haraji na sama da
Naira biliyan biyar.
Kamfanin ya ce watanni 24 ne lokacin da aka
amince kare kwangilar, amma ya ce ya kudiri
aniyar kammala wa a cikin watanni 16.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria ta kulla yarjejeniyar gina hanyar kankare da Dangote"

Post a Comment