Amurka ta nuna damuwa kan kisan 'yan Shi'a a Nigeria

Gwamnatin Amurka ta nuna damuwa game da
asarar rayukan da ake yi a Najeriya, sakamakon
arangama tsakanin `yan kungiyar `yan uwa
musulmi da jami`an tsaro.
Wata sanarwa da ofishin jakadancin kasar da ke
Najeriya ya fitar, ta ce akwai bukatar a dinga
samun fahimtar juna tsakanin mabiya kungiyar
da kuma mahukunta a Najeriya.
Amurka ta ce artabun da aka yi tsakanin `yan
sanda da `yan Shi'a, wadanda ke tattaki daga
Kano da nufin zuwa birnin Zazzau, a makon jiya,
abin takaici ne.
Amurka ta ce hankalinta ya tashi matuka da irin
karfin da `yan sanda suka yi amfani da shi a
karawar, duk cewa mahukunta a Najeriya na ci
gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.
Gwamnatin Amurkar ta bukaci `yan kungiyar da
kuma bangaren gwamnatin Najeriya da su kai
zuciya nesa, tare da mai da hankali wajen
tuntubar juna da nufin samun maslaha.
Sanarwar ta kara da cewa `yan kungiyar `yan
uwa musulmi suna da `yancin yin taro da sauran
hidimominsu na addini, kamar yadda kundin
tsarin mulkin Najeriya ya tanadar, amma a
bangare guda kuma wajibi ne su kasance masu
martaba dokar kasar.
Gwamnatin Amurkar ta bukaci mahukunta a
Najeriya da su gudanar da bincike na gaskiya da
gaskiya a kan wannan sabon rikicin da kuma
wani dauki-ba-dadin da sojoji suka yi da `yan
kungiyar `yan uwa musulmin a watan Disamban
bara, wanda ya yi sanadin mutuwar `yan kungiyar
sama da 300.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Amurka ta nuna damuwa kan kisan 'yan Shi'a a Nigeria"

Post a Comment