Iran za ta daure dan-dan Ayatollah Montazeri

A kasar Iran, an yanke wa dan-dan daya daga
cikin jiga-jigan mutanen da suka jagoranci juyin
juya-hali a kasar, hukuncin daurin shekaru shida
a gidan yari, saboda ya saki wani faifai, inda a
ciki, mahaifinsa ke yin Allah wadai da yadda
gwamnati ke karkashe firsinonin siyasa.
Kafofin yada labarai na kasar sun ce an samu
Ahmad Montazeri da laifin yin barazana ga
tsaron kasa, da yada farfaganda.
A watan Agusta ne, Mista Montazeri ya fitar da
muryar, inda aka ji mahaifin na shi, Ayatollah
Hossein Ali Montazeri, ya na sukar yadda aka
kashe dubban firsinoni a 1988.
An raba Ayatollah Montazeri da mukaminsa
saboda Allah wadai da kashe-kashen da ya yi,
kuma ya ci gaba da zama gaba-gaba wajen nuna
adawa har zuwa mutuwar shi a 2009.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Iran za ta daure dan-dan Ayatollah Montazeri"

Post a Comment