An dakatar da karin kudin data a Nigeria

Hukumar da ke sa ido a a kan kamfanonin
sadarwa ta Najeriya, NCC ta dakatar da shirinta
na kara kudin data ga masu amfani da wayar
salula.
Wata sanarwa da mai magana da yawun
hukumar, Tony Ojobo ya aikewa manema labarai,
ya ce sun dauki matakin ne sakamakon sukar da
suke sha daga wurin jama'a.
A cewarsa, hukumar ta umarci kamfanonin
sadarwa su dakatar da kara kudin datar kan
masu amfani da su.
A makon jiya ne hukumar ta bai wa kamfanonin
sanarwar umarnin kara kudin da suke sayar da
data zuwa kwabo 90 kan kowanne mega bite
daga ranar daya ga watan Disamba mai zuwa.
Sai dai 'yan Najeriya sun soki matakin, suna
maus cewa wani yunkuri ne na hana su fadar
albarkacin bakinsu.
Kafin a saoke karin zai shafi manyan kamfanoni
ne irin su MTN da Globacom da Airtell.
Haka kuma an yi niyyar rage farashin datar da
kananan kamfanoni.
A baya dai manyan kamfanonin na sayar da data
a kan: Etisalat N0.94k/MB, Airtel N0.52k/MB,
MTN N0.45k/MB da kuma Globacom N0.21k/MB.
Su kuma kananan kamfanoni na sayar da data a
kan: Smile Communications N0.84k/MB,
Spectranet N0.58k/MB da kuma NATCOMS
(NTEL) N0.72k/MB.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An dakatar da karin kudin data a Nigeria"

Post a Comment