Chadi: Mayakan Boko Haram sama da 1000 sun mika wuya

Mayakan Boko Haram fiye da 1000, 'yan asalin
kasar Chadi da suka je Najeriya domin yi wa
kungiyar yaki sun koma kasarsu tare da mika
wuya ga hukumomi.
Wani jami'in kasar, Dimouya Souapepe, ne ya
shaida wa BBC cewa, cikin mayakan har da mata
da yara, kuma sun mika wuya ne ga jami'an tsaro
tun watanni biyu da suka gabata.
Jami'in ya kara da cewa, ba wai ana tsare da su
ba ne, amma za a sake su zuwa ga 'yan uwansu
bayan an kammala bincike a kansu.
A wani bangaren kuma babban hafsan sojin
Najeriya Janar Tukur Buratai, ya ce kashi 60
cikin dari na mayakan Boko Haram ba daga
Najeriya suke ba.
Kafar yada labarai ta AllAfrica ta bayar da
rahoton cewa, Laftanar Janar Buratai ya yi
bayanin haka ne a wata tattaunawa da suka yi
da jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Maiduguri,
Mohammed Ibn Chambas.
Kungiyar Boko Haram dai ta yi barna sosai a
yankin kudu da sahara, inda ta yi sanadin
mutuwar dubban mutane, kuma ta kwace iko da
yankunan arewa maso gabashin Najeriya, da ma
wasu yankuna a kasashen da ke makwabtaka.
A halin da ake ciki yanzu dai kungiyar ta rasa iko
da yankuna da dama a bana, sakamakon taron
dangi na sojojin kasashen yankin tafkin Chadi da
ke makwabtaka da Najeriya..

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Chadi: Mayakan Boko Haram sama da 1000 sun mika wuya"

Post a Comment