Japan za ta ci gaba da hulda da Amurka

Shugaba Shinzo Abe na Japan ya gana da
zababben shugaban Amurka Donald Trump,
domin tattaunawa tare da fayyacewa kasar sa
kalaman da Mista Trump ya yi amfani da su a
lokacin yakin neman zabe.
Daga bisani bayan tattaunawar da shugabannin
biyu suka shafe tsahon mintina casa'in, wadda
aka yi ta a dogon ginin Trump Towers da ke
Manhattan.
Shugaba Abe ya shaidawa manema labarai cewa
tattaunawar da suka yi da Mista trump ta kara
masa karfin gwiwa, kuma a shirye kasar sa ta ke
dan kulla dangantaka mai dorewa tsakanin ta da
Amurka.
Japan dai ta nuna damuwa matuka a lokacin da
aka sanar da Mista Trump a matsayin sabon
shugaban Amurka, saboda rashin sanin tabbas
din ko kasashen biyu za su ci gaba da
kasancewa kawaye musamman da fuskar huldar
diplomasiyya da tsaro.
A lokacin da yake yakin neman zabe, mista
Trump ya ce dole kasashe kawayen Amurka su
shiga cikin taimakon da Amurka ke badawa, da
suka hada da biyan dakarun kawance na NATO
maimakon ita kadai ta dauki nauyin su.
A kuma wannan lokacin ya ce kamata ya yi
Japan ta samar da makamin nukiliya na kashin
kan ta, da kuma duba yiwuwar ci gaban
kasashen biyu ta fuskar kasuwanci.
A ranar 20 ga watan junairu ne Mista Trump zai
sha rantsuwar kama aiki, a kuma wannan ranar
ne wa'adin mulkin shugaba Barack Obama ke
zuwa karshe.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Japan za ta ci gaba da hulda da Amurka"

Post a Comment