Sojojin Nigeria sun mamaye Zamfara

Mazauna wasu yankuna na jihar Zamfara da ke
arewacin Najeriya sun ce an samu kwararar
dakarun sojin kasar dauke da manyan makamai
zuwa cikin jihar.
Mutanen da BBC ta yi hira da su sun ce ba su
saba ganin yawan sojojin da aka tura jihar ba.
Hakan dai na faruwa ne kwanaki kadan bayan
masu fashin shanu sun addabi jihar, lamarin da
ya kai ga kashe akalla mutum 150.
Barayin shanun sun fi addabar mazauna yankin
Dansadau da ke karamar hukumar Maru.
Wani mazaunin yankin, Malam Nuhu Dansadau,
ya shaida wa BBC, "Mun ga kananan jiragen yaki
uku - da wasu manya da motoci sama da 27
dauke da sojoji: wasu sun tafi yankin da aka
kashe masu hakar zinare, wasu kuma sun tsaya
a Magami da Dansadau. Mutanen yankin na cike
da murna."
Da ma dai gwamnatin kasar ta sha alwashin
murkusshe barayin shanun da suka addabi
yankin.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sojojin Nigeria sun mamaye Zamfara"

Post a Comment