An kai wa 'yan gudun hijirar Bama taimako

A Najeriya kungiyoyi da dama na ci gaba da
yunkurin tallafa wa 'yan gudun hijirar da rikicin
Boko Haram ya raba da gidajensu.
Duk da irin nasarorin da dakarun kasar da na
makwaftan kasashe suka samu na kwace
yawancin garuruwa da 'ya'yan kungiyar suke rike
da su a baya, har yanzu mafiya yawan wadanda
abin ya shafa na zaune ne a sansanoni daban-
daban da hukumomi suka kafa, inda kuma suke
ci gaba da kokawa kan halin kuncin da suke ciki.
A karshen mako wata tawagar kungiyar matan
sojijin sama na Najeriya, ta kai ziyara ga 'yan
gudun hijira da ke sansanin garin Bama a jihar
Borno, inda suka kai tallafin kayan abinci da na
bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijira.
Kimanin mutane dubu goma sha uku ne ke zaune
a sansanin 'yan gudun hijirar, wakilin BBC da ke
cikin tawagar ya rawaito yadda yara kanana da
mata da tsafoffi ke ta sowa da murna a lokacin
da tawagar ta isa da kayan tallafin.
Wata babbar matsala da 'yan gudun hijirar ke
fama da ita baya ga ta abinci, shi ne rashin
makewayi isassu, haka kuma akwai jama'ar da
ke kwana a sararin subahana ko dan tantin da
ake kafawa ba su samu ba.
Fatan mutanen dai shi ne zaman lafiya da
kwanciyar hankali su dore a Nigeria, a kuma
kawo karshen tada kayar baya na kungiyar Boko
Haram, wanda hakan ne zai ba su damar
komawa gidajensu dan ci gaba da rayuwa kamar
yadda aka saba a baya.
Tun a watan Maris din shekarar da ta wuce
dakarun Nigeria suka fatattaki mayakan Boko
Haram daga garin na Bama, sai dai har yanzu
jama'ar da suka yi gudun hijira ba su samu
damar komawa gidajen su ba.
Abin tambayar anan shi ne ko za a dore wajen ci
gaba da kai wa mutanen kayan agaji?

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kai wa 'yan gudun hijirar Bama taimako"

Post a Comment