Mutmin da yafi kowa kiba a duniya na kwance a asibiti

An kwantar da mutumin da ya fi kowa nauyi a
duniya, Juan Pedro Franco, a asibiti bayan da ya
kasa tafiya saboda nauyinsa ya kai sama da
kilogram 500.
Mista Pedra, mai shekara 32 ya kwashe mafi
yawan lokuta a shekara 15 da yayi a cikin wani
karamin gado a gidansa da ke birnin
Aguascalientes na Mexico.
Kibarsa ta karu ne bayan ya kamu da cutar
nimoniya da hatsarin da ya yi a lokacin da yana
matashi lamarin da yasa shi jin jinyar sama da
shekara guda.
Ya kara nauyi sama da kilogram 95 a cikin
watanni hudu kawai tun bayan da ya nemi
taimakon kudi domin ya sauya irin abincin da ya
ke ci.
Dakta Jose Antonio Castaneda Cruz, na daga
cikin tawagar likitocin da za su kula da Mista
Pedro a asibitin Jardines da ke Guadalajara.
Ana bukatar ya rage kilogram 45 na nauyinsa
kafin a yi masa tiyata.
Matsananciyar tebar da yake da ita ta sa mai
yiwu wa ya doke dan kasar Mexico Manuel Uribe,
a matsayin mtumin da ya fi kowa nauyi a duniya.
Mista Uribe, mai shekara 48, ya mutu yana da
nauyin kusan kilogram 600 a shekarar 2014.
An yi amfani da na'urori na musamman wajen
daukar Juan Pedro ciki har da ta taimakawa
wajen yin numfashi kafin a kai shi asibiti.
Mista Pedro, mai buga na'urar jita ya nemi
taimako a watan Yuli a lokacin da nauyinsa ya
haura kilogram 381, inda ya bayyana cewa ya
shafe shekara shida bai bar dankisa ba bayan ya
bar cin abinci na mussaman lokacin da iyayensa
'yan fansho suka kasa saya masa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mutmin da yafi kowa kiba a duniya na kwance a asibiti"

Post a Comment