Messi da tawagarsa sun yi wa 'yan jarida bore

Lionel Messi ya jagoranci 'yan wasan Argentina
domin kin yin hira da 'yan jarida saboda
rahotanni "marasa dadi" da suka wallafa a kan
tawagar kwallon kafar kasar.
Dan wasan mai shekara 29 ya bayyana cewa ba
za su yi hira da 'yan jarida ba bayan an kammala
wasan cancantar shiga gasar cin kofin duniya
inda suka doke Colombia da 3-0.
Wani rahoto da 'yan jarida suka wallafa ya yi
zargin cewa dan wasan gaba Ezequiel Lavezzi ya
sha tabar wiwi bayan sun yi atisaye, kodayake ya
musanta zargin.
Messi ya ce, "Mun sha suka daga wajen 'yan
jarida, kuma yawancin abubuwan da ake fada a
kan mu na rashin da'a ne amma ba mu ce komai
ba."
Messi da sauran 'yan wasan 25 sun yi banza da
'yan jarida bayan an kammala wasan.
An bayyana cewa Lavezzi zai kai gurfanar da dan
jaridar da ya zarge shi da shan wiwi a kotu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Messi da tawagarsa sun yi wa 'yan jarida bore"

Post a Comment