An bukaci a daure Eto'o shekara 10

Masu gabatar da kara a Spaniya sun nemi kotu
ta daure tsohon dan wasan Barcelona da kamaru
Samuel Eto'o, sama da shekara 10 kan kin biyan
haraji.
Suna zarginsa ne da kafa kamfanoni da yawa
domin ya kauce wa biyan haraji lokacin da yake
Barcelona, daga 2004 zuwa 2009.
Bayan hukuncin daurin shekara goma da wata
shida masu gabatar da karar suna kuma son kotu
ta ci tsohon dan wasan na Barcelona
tarar dala miliyan 15 da dubu 100 bisa laifuka
hudu da suke zarginsa na kin biyan harajin dala
miliyan hudu a shekarun da ya yi a kungiyar
Masu gabatar da karar suna kuma neman a
yanke wa wakilin dan wasan a lokacin da yake
kungiyar Jose Maria Mesalles irin wannan
hukunci.
Ba a dai samu jin ta bakin Eto'o da lauyoyinsa ba
kan zargin, amma tun a baya dan wasan ya taba
musanta yin wani abu ba daidai ba game da
biyan harajin.
Eto'o na daga cikin 'yan wasan Barcelona na da
da na yanzu da suke fuskantar shari'a a Spain.
is among other current and past Barcelona
players facing legal problems in Spain.
A watan Yuli, an yanke wa Lionel Messi da
mahaifinsa hukuncin zaman gidan yari na wata
21 bisa laifin kin biyan haraji.
Sai dai ba a tura su gidan mazan ba, saboda bisa
dokokin Spain idan wa'adin yari bai kai shekara
biyu ba a masu laifi karon farko za a iya dage
shi.
A yanzu Neymar da mahaifinsa da Barcelona ma
na fuskantar shari'a daga hukumomin Spain kan
zargin almundahana a cinikin dan wasan na
Brazil daga Santos a 20134.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An bukaci a daure Eto'o shekara 10"

Post a Comment