Mahrez: Ba na son tunanin faduwa daga Premier

Dan wasan gefe na Leicester City Riyad Mahrez
ya ce ba ya son yin tunanin faduwa daga
Premier bayan da zakarun suka yi rashin nasara
a karo na shida a bana.
A ranar Asabar ne Watford ta ci su 2-1, kuma a
yanzu suna matsayi na 14 a tebur da maki 12 a
wasa 12, maki biyu tsakaninsu da rukunin masu
ficewa daga gasar.
Dan wasan ya ce, ''ba wata matsala. Muna
bukatar mu ci gaba da aiki tukuru ne kamar
yadda muka yi, kuma na tabbata za mu dawo cin
wasanninmu,''
''Na san cewa muna da kyawun da za mu tsaya a
Premier, ko ma fin hakan.''
Sabanin matsayinsu a gasar ta Premier, kungiyar
na gab da samun kaiwa matakin 'yan 16 na cin
kofin Zakarun Turai a shigarsu ta farko gasar.
Kawo yanzu sun yi nasara sau uku, da canjaras
daya a wasanninsu hudu na rukuni, ba tare da an
zura musu kwallo ko daya ba, kuma za su kara
da Club Brugge ranar Talata.
Mahrez ya ce, ''bara bara ce, mu ne zakaru.
Amma ko mu zakaru ne ko ba zakaru ba ne,
wannan wata shekarar ce daban.
''Sauran kungiyoyi sun fi mu buri, kuma kowace
kungiya burinta shi ne ta doke Leicester. Saboda
haka dole ne mu kokarta, kuma na san za mu
dawo ganiyarmu.''
Sunan Mahrez na cikini jerin 'yan wasa 23 da za
a zabi gwarzon dan wasan hukumar kwallon kafa
ta duniya Fifa na 2016 a cikinsu, amma kuma ya
kawar da yuwuwar samun matsayin.
Ya ce, ''akwai manyan 'yan wasan da suka fi ni.
Ni dai farin cikina kawai shi ne da sunana a ciki,''

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mahrez: Ba na son tunanin faduwa daga Premier"

Post a Comment