Kotu za ta yanke wa 'Hyena' hukunci cikin watannan

 kotun kasar Malawi, ta samu mutumin da
ya shaida wa BBC ya sadu da mata 104 alhalin
yana dauke da cutar HIV ko Sida, da laifin yin
lalata da yara. Kotun ta samu Eric Aniva da
laifin aikata mummunar al'ada, da tilastawa
amare da matan da mazajen su suka rasu yin
jima'i.
A wata hira da ya yi da BBC gabannin yanke
masa hukuncin, mista Eric ya kuma ce ya na
wannan dabi'a ga kananan yara 'yan shekara 12,
dan shiryawa lokacin budurcin su kamar yadda
al'adar yankin da ya fito ta amince da yi.
Asirin Eric Aniva da ke wa lakabi da Kura ko
Hyena a turance ya tonu ne, bayan wata hira da
ya yi da BBC, inda ya bayyana aika-aikar da ya
ke da sunan al'ada alhalin ya na dauke da cutar
Kanjamau ba kuma tare da ya sanar da iyayen
'yan matan da matan da ke takaba ba.
Gwamnatin kasar Malawi ce da kanta ta bada
izinin cafke Mista Eric, a wani mataki da ba a
sabar ganin an dauka ba a kasar. kotun dai ta
same shi da laifi karkashin dokokin Malawi da
suka shafi Jinsi, cikin laifukan na sa akwai, yin
lalata da kananan yara, da sunan mutunta al'ada,
bayan wasu mata biyu sun shaidawa kotu cewa
'yan uwan su ne suka biya Mista Eric dan ya yi
jima'i da wasu kananan yara alhalin ya na dauke
da kwayar cutar HIV.
Batun aika-aikar da Mista Eric ya yi dai ya ja
hankalin kasashen duniya, an kuma yi zazzafar
muhawara a ciki da wajen kasar kan ci gaba da
yin wannan mummunar al'ada ko kuma gwamnati
ta soke ta baki daya.
A ranar 22 ga wannan watan ne za a yanke
masa hukuncin da ya dace da laifin da ya aikata.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kotu za ta yanke wa 'Hyena' hukunci cikin watannan"

Post a Comment