An kira Michelle Obama biranya

Wata shugabar birni ta yi murabus a jihar West
Virginia da ke Amurka bayan ta kwatanta matar
Obama, Michelle Obama da biranya.
Beverly Whaling dai ta yaba wa wani sako da aka
wallafa a shafin facebook inda aka bayyana Mrs
Obama a matsayin "biranya sanye da takalmi
mai tsayi"
Ta rubuta cewa sakon da aka wallafa ya sa ta ji
dadin ranar, amma kuma daga baya sai ta mayar
da martani kan sakamakon zaben Amurka.
Mutum 170,000 ne dai suka sanya hannu a wani
korafi inda suka bukaci shugabar birnin ta yi
murabus.
Ms Whaling ce dai shugabar birnin Clay, wanda
ke da yawan mutane 491 kafin ta yi murabus.
A cewar kididdigar shekarar 2010, garin ba shi
da mazauna, Amurkawa 'yan asalin Afirka.
A baki daya garin Clay, sama da kashi 98 cikin
100 na mazauna su 9,000 da garin Turawa ne

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kira Michelle Obama biranya"

Post a Comment