Klopp: Coutinho na nan daram a Liverpool

Kocin Liverpool ya ce Philippe Coutinho zai ci
gaba da zama daram a Anfield sakamakon rade
radin da ake yi cewa gwanin dan wasan zai bar
kungiyar.
Dan wasan na Brazil mai shekara 22, ya taimaka
wa kungiyar ta kai matsayin da take yanzu a
teburin Premier, inda ya ci kwallo biyar, kuma ya
bayar aka ci biyar.
Saboda tashen da yake yi a yanzu, shi ne ake
rade radin cewa zai koma kungiyar Barcelona ko
Real Madrid.
Jurgen Klopp ya ce, ''a ra'ayina ni dai dan wasan
ya dace sosai da nan (Liverpool).''
Ya ce, ''dukkaninmu muna fata tare da ganin
cewa damarsa na nan Liverpool. Abin da mutane
ke mantawa da shi a kan Phil shi ne, har yanzu
matashi ne.
A matsayinsa na dan shekara 24, yana da sauran
aiki a gabansa, yana bukatar samun kwarewa
sosai.''
Rabon da Liverpool ta fara gasar Premier da
kyau kamar bana tun kakar 2008-09, inda yanzu
take ta daya da maki 26 da kwallo 30 a wasa 11.
Kungiyar za ta yi wasanta na Premier na gaba a
gidan Southampton, ranara Asabar.
Klopp bai damu da kudin da manyan kungiyoyin
Turai ke zuba wa domin sayen 'yan wasa ba, da
za su iya janye 'yan wasansa ba.
Ya ce, '' maganar ba ta kudi ba ce. Idan da
kungiyar da za ta biya dan wasa linki biyun abin
da muke biya, sai in sayar musu da dan wasa.''
Kocin dan Jamus ya kara da cewa, ''wanene ni
da zan ce dan wasa kada ya yi tunanin iyalinsa,
ko 'ya'yansa, ko jikokinsa, ko sauransu, amma
dai ban ga wasu kungiyoyi da yawa a duniya da
za su iya yin haka ba.''
Ya ce, ''muna samar da yanayi na yadda ba
wanda zai so ya bar kungiyar, kuma a yanzu ba
ni da wata fargaba, domin 'yan wasan na son
zama a nan.''

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Klopp: Coutinho na nan daram a Liverpool"

Post a Comment