Kasashen Turai za su bai wa Birtaniya mamaki

Firai ministan Malta ya ce ba wasa suke yi ba
da suka ce ba za su bari Birtaniya ta rika
kasuwanci da su ba tare da ta biya haraji ba
kuma ta hana 'yan kasashensu shiga cikin ta ba
tare da shamaki ba bayan ta fice daga Tarayyar
Turai.
Joseph Muscat, wanda kasarsa za ta karbi
shugabancin kungiyar Tarayyar Turai a watan
Janairu, ya shaida wa BBC cewa "wannan shi ne
hakikanin matsayinmu kuma ba za mu sauya
ba".
Firai ministar Birtaniya Theresa May ta ce
kasarta za ta soma shirye-shiryen ficewa daga
Tarayyar Turan a watan Maris.
Amma Mr Muscat ya ce za a iya jinkirta
tattaunawa kan sabuwar dangantakar da za ta
kasance tsakanin Birtaniya da kasashen Tarayyar
Turan.
Yawancin hasashen da aka rika yi ya ta'allaka ne
kan yadda Birtaniya za ta fice daga Turai salin-
alin ta yadda za a bar ta ta rika kasuwanci da
sauran kasashe ba tare da ta biya haraji ba,
yayin da ita kuma za ta yi sassauci kan dokokin
shige-da-ficenta.
Sai dai Mr Muscat ya ce dole ne Birtaniya da
kasashen Tarayyar Turan su amince da sababbin
sharuddan dangantaka a tsakaninsu kafin, a
hukumance, Mrs May ta sanar da su kasarta za
ta fice daga tarayyar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Kasashen Turai za su bai wa Birtaniya mamaki"

Post a Comment