Sakamakon zaben Amurka ya gigita ni - Clinton

A karon farko Hillary Clinton ta fito fili ta
bayyana irin takaicinta a kan shan kayen da ta yi
a hannun Donald Trump a zaben kasar da aka yi
a makon jiya.
Misis Clinton ta ce sai da ta ji kamar ta hada
kanta da gwiwarta ta rufe a cikin wani "littafi
sannan na ki fitowa daga gida har abada".
Sai dai a wani jawabi da ta yi a wurin wata
gidauniyar yara marasa galihu, Misis Clinton ta yi
kira ga mahalarta taron da su zage dantse domin
yaki wajen kare martabar muradun Amurka kuma
kada su taba karaya.
'Yar takarar jam'iyyar Democrat din dai ita ce ta
lashe yawancin kuri'un da aka kada a zaben, sai
dai Mista Trump ya fi ta yawan wakilan da suke
zabar shugaban kasar, abin da ya sa ya yi
nasara.
Misis Clinton ta shaida wa mahalarta taron cewa,
"A gaskiya zan fada muku cewa ba na yi kokari
sosai kafin na iya zuwa nan. Na san yawancin ku
ba ku ji dadin sakamakon zaben ba. Ni ma ban ji
ba, fiye da yadda kuke tsammani
"Na san hakan na da matukar wuya. Na san
cewa mutane da dama sun kashe tsawon
wannan mako suna tambayar cewa anya wannan
ita ce kasar Amurkan da muke tunani."
Mahalarta taron sun yi ta jinjina mata, suna
masu cewa gwiwoyinsu ba su yi sanyi ba.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Sakamakon zaben Amurka ya gigita ni - Clinton"

Post a Comment