An kawo karshen dokar ta baci kan Zika- WHO

Hukumar lafiya ta duniya ta janye dokar ta bacin
da aka ayyana akan cutar Zika saboda a yanzu
an shawo kan matsalar.
Duk da wannan sanarwa, ma'aikatar lafiya ta
kasar Brazil ta ce za ta ci gaba zage dantse dan
magance cutar saboda irin illar da ta ke yiwa
jarirai a cikin mahaifiyarsu.
Brazil dai na daga cikin kasashen da cutar Zika
ta fi yaduwa tsakanin mata masu juna biyu,
wadda ke janyo haifar jarirai da tawaya a
kwakwalwarsu da dan karamin kai.
Likitocin sun bayyana cutar a matsayin annoba,
kuma wasu sun shawarci mata a kasashen da
cutar ta bulla, da su jinkirta daukan ciki.
A kwanakin baya ne wasu kwararru a kan kiwon
lafiya daga Amurka da kasashen Latin Amurka
da Karebiyan fiye da talatin, suka yi taron koli na
farko a kan yadda za a tunkari cutar ta Zika.
Masana kimiyya da Kungiyar lafiya ta Duniya-
WHO, na ganin sauron da ke dauke da cutar ne
ake alakantawa da cutar da haddasa haihuwar
gilu.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An kawo karshen dokar ta baci kan Zika- WHO"

Post a Comment