An yi Shari'ar farko ta 'yan luwadi a Ivory Coast

Hukumomin Ivory Coast sun yi shari'ar farko ta
'yan luwadi biyu a kasar, inda aka yanke musu
zaman gidan sarka na watanni goma sha
takwas.
Kafafen watsa labarai na kasar ba su bayyana
sunayen mutanen biyu ba, inda aka yi musu
inkiya da, P.L., mai shekara 31 da kuma L.A.,
mai shekara 19, wadanda suka fito daga wani
kauye a kudu-maso-yammacin kasar.
Kawun karamin daga cikinsu ne ya gan su
lokacin da suke saduwar, kuma nan da nan ya
kai rahotonsu gun 'yan sanda.
Mutanen biyu sun amince cewa suna soyayya ta
luwadi a junansu, amma kuma sun ce, su ba su
san cewa hakan laifi ne ba, kamar yadda rahoton
jaridar intanet ta Abidjan.net ta bayyana.
Ba a haramta luwadi a kasar ta Ivory Coast ba,
amma laifi ne a yi wani abu da ya shafi luwadi a
bayyanar jama'a.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An yi Shari'ar farko ta 'yan luwadi a Ivory Coast"

Post a Comment