Hanyoyi 6 da zaku iya gane shinkafar bogi

Rahotannin da ke yawo suna nuna cewar
wasu bata gari daga kasar Sin watau China
sun fara cika kasuwannin kasashen Afrika
ciki kuwa hadda Najeriya da wata samfurin
shinkafar bogi ta roba
– Ita dai kasar ta Sin ta yi kaurin suna
wajen samar da kayayyakin anfani na bogi
ciki kuwa hadda kayayyakin abinci
Shinkafa
Tun farko dai wata jaridar kasar Korea ce ta
fara bankado labarin na wasu yan kasar
China din da ke kera shinkafar roba kuma
tuni har sun fara rarraba ta a kasashen
duniya musamman ma a Afrika.
Ga wasu hanyoyi nan har guda 6 da
amintaccen kamfanin jaridar nan taku na
NAIJ.com ya zakulo maku don anfanin
kawunan mu kan hanyar da za’a bi wajen
gane shinkafar ta boji. Gasu a kasa:
1. Hanyar turmi da tabarya
Idan ku ka samu shinkafar ku sai ku dan
daka ta a cikin turmi da tabarya, idan har ta
dan yi farin gari to tabbas wannan shinkafar
ta kwarai ce mai kyau amma idan kuka ga
wani koriyar kala tana fita daga gare ta to
tabbas shinkafar bogi ce. Sai a kiyaye.
2. Gwaji da wuta
Ai ina fata dai duk munsan yadda kaurin roba
yake idan ana kona ta ko? To hakan ne ma
ake yin wannan kwagin. Idan kuka samu
shinkafar sai a nan kona ta, idan har ta
kama da wuta kuma aka ji kaurin to tabbas
tanan ma za a iya tantancewa.
3. Gwaji a cikin ruwa
Idan muka samu kofi da ruwa a ciki sai a
nan dibi shinkafar da ake kokwanto a zuba a
cikin kofin. Idan har shinkafar ta nutse a
cikin ruwan to tabbas tana da kyau da
inganci, idan kuwa akasin haka ya faru to
tabbas ta bogi ce.
4. Gwajin dambada
Yadda ake wannan gwajin kuma shine a
samu shinkafar da ake kokwanto sai a dan
dafa ta kadan sai a tsameta abarta a wani
wuri mai lema ta kwana kamar 2 zuwa 3.
Idan har tayi hunhuna to tana da kyau
kenan.
5. Ta hanyar tafasawa
Idan ana tafasa shinkafar da ake kokwanton
sai a kula da irin kumfan da ke fita a jikin
tukunyar. Idan har kuka ga kumfan da takeyi
ya wuce misali, to tabbas shinkafar ta bogi
ce.
6. Gwaji ta hanyar tafasashen mai
Sai a samu shinkafar da ake kokwanton
ingancin ta sai a samu tafasasshen mai a
zuba shinkafar a ciki. Idan har ta roba ce to
za kuga ta fara narkewa sannan kuma tana
hadewa da juna.
Idan har hakan ta faru, sai
a kiyaye, shinkafar ta bogi ce.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Hanyoyi 6 da zaku iya gane shinkafar bogi"

Post a Comment