'An buga hotunan Wayne Rooney ya yi mankas da giya'

Kyaftin din Ingila Wayne Rooney ya nemi afuwar
kocin tawagar kwallon kafar kasar na riko Gareth
Southgate bayan an fitar da wasu hotuna da ke
nuna shi a wajen wani biki a otal din da tawagar
kasar ke zaune.
Wata sanarwa da aka fitar a madadinsa ta ce
Rooney, mai shekara 31, ya amince cewa
hotunan ba su dace ba.
Jaridar The Sun ta wallafa hotunan da ta ce sun
nuna Rooney ya bugu da giya a wajen wani biki
da tsakar daren ranar Asabar - kwana daya
bayan Ingila ta doke Scotland a wasan cancantar
shiga gasar cin kofin duniya.
A waje guda kuma, hukumar kwallon kafar Ingila,
FA, ta ce tana duba yiwuwar yin sauye-sauye ga
dokar barin 'yan wasa suna amfani da lokutan
hutunsu.
Jaridar The Sun ta ce FA za ta yi sauye-sauyen
ne saboda 10 daga cikin 'yan wasan Ingila sun
tafi gidan sharholiya inda suka kai har karfe
04:30 na asubahin ranar Lahadi bayan wasan da
suka yi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'An buga hotunan Wayne Rooney ya yi mankas da giya'"

Post a Comment