Facebook zai magance matsalar wallafa labaran bogi

Kamfanin Facebook ya sanar da wasu sabbin
matakai na rage yawan labarai na bogi da ake
wallafawa a shafin sa.
A wani sako daya wallafa, shugaban kamfanin
Mark Zuckerberg ya ce Facebook na bullo da
wasu sabbin hanyoyi tantance labarai na bogi
inda yake duba yiwuwar kafa wata hukuma ta
tantance labarai na gaskiya.
Facebook dai ya yi ta shan suka akan yawan
labarai na bogi da aka rika wallafawa a shafin sa
gabannin zaben Amurka wanda ake zargin cewa,
irin labaran da aka rika wallafawa sun taimaka
kan yadda sakamakon zaben ya kasance.
A ranar asabar ne Mr Zuckerberg ya yi jawabi ga
shugabannin kasashen duniya dake halartar taron
APEC a Peru, inda ya bukace su da su yi aiki
tare wajen ganin an hada duniya wuri guda ta
fuskar samar da hanyoyin Internet don magance
talauci tsakanin mutane biliyan 4 da basu da
damar amfani da Internet.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Facebook zai magance matsalar wallafa labaran bogi"

Post a Comment