'Matasan N-Power za su fara karbar albashi a Disamba'
Mai taimakawa mataimakin shugaban Najeriya,
ofishin da ke kula da alhakin shirin samawa
matasa aiki na N-Power, Hafiz Ibrahim, ya ce
matasa dubu 200 da aka dauka aiki ba za su
fuskanci matsalar albashi ba.
A ranar Alhamis din nan ne dai ake sa ran shirin
na N-Power zai fara aiki.
Hafiz ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC, a
inda ya ce shirin na N-Power, ba zai zama kamar
sauran ayyukan gwamnati ba da ake daukar
ma'aikata ba tare da albashi ba har na tsawon
watanni.
Ya ce matasan da aka dauka za su dauki albashi
a watan farko na fara aikinsu wato Disamba.
Ya kuma kara da cewa gwamnati ta rigaya ta
kebe kudade a kasafin kudin kasar wadanda da
su ne za a biya matasan.
Sai dai kuma wasu matasan da suka samu aikin
na N-Power wadanda kuma suka zanta da BBC,
sun ce duk da cewa yau ne ake fara shirin amma
su kam ba su san inda za su je ba domin fara
aiki.
To amma Hafiz Ibrahim ya ce, ranar farko ta fara
wannan shiri za ta zama lokacin sake tantance
matasan domin gane unguwowinsu da
garuruwansu, kafin daga bisani a fada musu
wurin da za su je aiki.
A watan jiya ne dai gwamnatin Najeriya ta fitar
da jerin sunayen matasa dubu 200 da ta ce sun
samu nasarar shiga kashin farko na shirin na N-
Power.
Matasa dubu 150 ne aka dauka a matsayin
malaman makaranta.
Dubu 30 kuma za su yi aiki a fannin noma, yayin
da ragowar dubu 20 din za su yi aiki a fannin
kiwon lafiya.
Miliyoyin matasa ne dai a kasar ke fama da
rashin aikin yi.
Kuma 'yan kasar sun zura ido domin ganin yadda
gwamnatin Muhammadu Buhari za ta shawo kan
wannan matsala.
Magance matsalar aikin yi dai na daya daga cikin
batutuwan da shugaba Buharin ya yi alkawarin
magancewa lokacin yakin neman zabensa.
Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin matasa
miliyan 70 daga cikin mutanen Najeriya miliyan
167.

0 Response to "'Matasan N-Power za su fara karbar albashi a Disamba'"
Post a Comment