An zartar da hukuncin kisa kan dan Nigeria a Singapore

Hukumomi a kasar Singapore sun ce sun kashe
mutum biyu - dan Najeriya da dan Malaysia -
bayan sun kama su da laifin yin safarar miyagun
kwayoyi.
Wata sanarwa da hukumar da ke yaki da safarar
miyagun kwayoyi ta kasar ta fitar ta ce an kashe
Chijioke Stephen Obioha a gidan yarin Changi
ranar Juma'a.
Ta kara da cewa an same shi ne da laifin yin
safarar tabar wiwi mai nauyin giram 2,604.56 a
shekarar 2008.
Shi kuma dan kasar Malaysia, Devendran
Supramaniam, ya shiga hannun jami'an tsaro ne
a shekarar 2011 saboda yunkurin shiga kasar da
hodar ibilis mai nauyin gram 83.36.
Lauyan Obioha da kungiyar kare hakkin dan
adam ta Amnesty International dai sun yi ta
fafutikar ganin ba a aiwatar da hukuncin kisa a
kansa ba.
Dokokin kasar Singapore sun amince a kashe duk
mutumin da aka kama da fiye da gram 500 na
wiwi.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An zartar da hukuncin kisa kan dan Nigeria a Singapore"

Post a Comment