Tinubu gagarabadan jam'iyar APC ne - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi
watsi da jita-jitar cewa shi da wasu shugabannin
jam'iyar APC suna takun saka da daya daga
cikin kusoshin jam'iyar Asiwaju Bola Tinubu.
Shugaba Buharin ya bayyana cewa irin wannan
jita-jita ba ta da tushe ballantana makama.
Babban mai bai wa shugaban kasar shawara kan
harkokin yada labarai Malam Garba Shehu, ya ce
shugaban kasar ya nuna matukar bacin ransa
game da batun.
Ya ce shugaba Buhari ya sha tattaunawa da Bola
Tinubu tun kafin lokacin zaben gwamnan jihar
Ondo da kuma bayan zaben.
Tun bayan sabanin da aka samu a zaben fitar da
gwani na jam'iyyar a jihar Ondo, rashin jituwa
take kara fitowa fili a jam'iyyar.
Hakan ne ya sa wasu ke zargin cewa magoya
bayan Buhari na kokarin ganin bayan Tinubu,
wanda shi ne ya jagoranci kafa jam'iyyar.
Malam Garba Shehun ya kara da cewa duk wani
shaci-fadin da ake yi cewa shugaban kasa da
'ya'yan jam'iyyar na yunkurin ganin bayan Tinubu,
ba shi da tushe.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ya dauki Tinubu
a matsayin wani gagarabadan dan siyasa, wanda
kowa ya san irin gagarumar gudummawar da
yake bayar wa wajen cigaban jam'iyya mai
mulki.
Malam Garba Shehu ya shawarci masu jita-jita
da su daina kokarin ganin kawo cikas tsakanin
shugaban kasa da Tinubu ko kuma jam'iyya.
Ya ce shugaba Buhari na alfahari da
''Jagaba'' (Tinubu) da kuma rawar da yake
takawa a cikin jam'iyyar.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Tinubu gagarabadan jam'iyar APC ne - Buhari"

Post a Comment