Mata ta kai ƙara kan ganin mushen ɓera a sabuwar rigarta

Wata mata a birnin New York na Amurka, ta
gano wani mataccen bera da aka dinke a cikin
wata sabuwar riga da ta saya.
Matar mai suna Cailey Fiesel ta ce ta sayo wata
riga ta dala 40 a kamfanin sayar da tufafi, Zara,
amma kuma bayan 'yan makonni tana zaune a
wurin aikinta sai ta rika jin wani doyi a jikinta.
Ms Fiesel, mai shekara 24, ta ce ta ji dan wani
abu ya karce ta a kafa, da ta duba sai ta ga
kafar bera ta dan leko daga lafin rigar tata.
Ta ce, '' sai kawai na kame, na suma a tsaye,
ban san ta yi ba, ina cike da tsoro,'' kamar yadda
ta sheda wa jaridar New York Post.
Matar dai ta shigar da kara a kan kantin na sayar
da tufafi mai cibiya a Spaniya, Zara.
Lauyoyin Ms Fiesel sun yi zargin cewa matar ta
yi fama da matsalar damuwa sannan kuma wasu
kuraje sun fito mata, wadanda likitoci suka
danganta da bera.
Kakakin kantin na Zara, reshen Amurka ya ce,
kamfanin yana sane da karar kuma suna gudanar
da bincike a kai.
Ya ce, Zara USA, yana da tsauraran dokoki da
tsare-tsare na tabbatar da ganin kayansa sun
kiyaye da ka'idoji.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Mata ta kai ƙara kan ganin mushen ɓera a sabuwar rigarta"

Post a Comment