'Facebook zai ba China damar tace bayanai a shafinsa'

Wani rahoto da jaridar New York Times ta
wallafa ya ce shafin sada zumunta na Facebook
na tsara wata sabuwar manhaja wadda ake iya
amfani da ita wajen hana wasu bayanai bayyana
a shafukan mutane a wasu sassan duniya.
Wasu jami'an kamfanin Facebook din uku sun
shaida wa jaridar cewa an tsara manhajar ne
domin taimaka wa kamfanin samun karbuwa a
kasar China.
Kodayake sun ce mai yiwuwa ba za yi amfani da
ita ba daga karshe, wanda ya kirkiro da shafin
dai Mark Zuckerberg ya kwashe lokaci mai tsawo
yana hulda da shugaban kasar ta China, Xi
Jinping, har ma ya daukar wa kansa koyon
harshen sinanci.
Kawo yanzu dai kamfanin na facebook bai
tabbatar ko musanta samar da wannan manhajar
ba, amma dai ya tabbatar da cewa yana kara
karantar kasar ta China.
Martani
Wata kungiyar masu kare hakkin masu amfani da
shafukan internet ta bayyana samun wannan
labarin a zaman ''abin damuwa matuka.''
Kungiyar ta Electronic Frontier Foundation,
wadda ke fafutukar inganta kiyaye sirrin masu
amfani da internet ta shaidawa BBC ta bakin
wani jami'inta Eva Galperin cewa; suna yabawa
ma'aikatan kamfanin na Facebook wadanda suka
tsegunta wa jaridar ta New York Times wannan
labari.
Rahotanni dai sun ambato Mr. Zuckerberg na
umartar yaransa da su kirkiro da wata manhaja
wadda za ta bai wa wani daga waje damar tace
bayanan da ka iya bayyana a shafukan mutane.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "'Facebook zai ba China damar tace bayanai a shafinsa'"

Post a Comment