Biri ya haddasa mummunar rikici a Libya

Jami'ai da masu fafutika a kasar Libya sun ce
wani Biri ya haddasa mummunar artabu tsakanin
wasu kabilu biyu da ke kasar.
Kawo yanzu babu cikakken bayani game da
lamarin, sai dai wasu majiyoyi a jihar Sabha dake
kudancin kasar sunce rikici ya barke ne bayan da
Birin na wasu mutane daga wata kabila ya
abkawa wasu yara mata 'yan makaranta na wata
kabila dake yankin.
Hakan dai ya haddasa kashe kashe na ramuwar
gayya, lamarin daya kaiga har aka kwashe
kwanaki hudu ana bata kashi.
Rahotanni sun ce akalla mutane 16 ne suka mutu
yayin da wasu da dama suka jikkata a wannan
rikici da Biri ya haddasa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Biri ya haddasa mummunar rikici a Libya"

Post a Comment