Nigeria: An kashe 'yan sanda 128 cikin wata uku

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ya ce
jami'ansa 128 ne suka mutu sakamakon hare-
haren da masu tsattsauran ra'ayi suka kai musu
a bakin-aikinsu.
Wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan
kasar DCP Don N Awunah ya aike wa manema
labarai ta ce an kashe jami'an 'yan sandan ne a
sassa daban-daban cikin wata uku.
Sanarwar ta ambato Babban Sufeton 'yan sandan
Ibrahim K. Idris yana bayyana hakan a matsayin
wani abu "mai matukar tayar da hankali".
Ya kara da cewa "wani abin takacin kuma shi ne
yadda ake rusa ofisoshin 'yan sanda da
kaddarorin mutane.
Sanarwar ta bayyana cewa a kwanakin baya an
kashe 'yan sanda a kauyen Dankamoji na
karamar hukumar Maradu da ke jihar Zamfara,
da garin Abagana da ke Anambra da kuma
Okrika da ke Ribas.
Rundunar 'yan sandan ta sha alwashin yin bakin
kokarinta domin kula da iyalan jami'anta da aka
kashe.
Ta yi kira ga 'yan kasar na gari su taimaka wa
'yan sanda idan suka gan su a irin wannan hali.
Sharhi - Nasidi Adamu Yahaya - BBC Abuja
A 'yan kwanakin nan dai ana ci gaba da samun
taho-mu-gama tsakanin 'yan sanda da wasu
kungiyoyi.
Ko da a farkon watannan sai da 'yan sandan
suka yi artabu da `yan kungiyar `yan uwa
musulmi a jihar Kano da ke arewacin kasar,
lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani dan
sanda da kuma mabiya kungiyar da dama.
A lokuta da dama ana zargin 'yan sandan da yin
amfani da karfin da ya wuce kima idan sabani ya
shiga tsakaninsu da jama'a.
Hakan ne ma ya sa a kwanakin baya Amurka ta
nuna damuwa game da asarar rayukan da ake yi
a Najeriya, sakamakon arangama tsakanin `yan
kungiyar `yan uwa musulmi da jami`an tsaro.
Sai dai 'yan sandan sun sha cewa suna daukar
mataki irin wannan ne domin kare kansu.
Baya ga 'yan sanda, sauran jami'an tsaro da
suka hada da sojoji da na kwastam su ma suna
fuskantar irin wadannan matsaloli.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Nigeria: An kashe 'yan sanda 128 cikin wata uku"

Post a Comment