Zaben 2019: 'Atiku da El-Rufai na sha'awar takara'

Masana harkokin siyasa a Najeriya sun ce
rikicin da ya barke tsakanin tsohon mataimakin
Shugaban kasar Atiku Abubakar da Gwamna
Nasir El-Rufai na jihar Kaduna wata alama ce da
ke nuna cewa an soma buga gangar siyasar
shekarar 2019.
Ce-ce-ku-ce ya barke tsakanin jiga-jigan
jam'iyyar ta APC mai mulkin ne sakamakon
zargin da suke yi wa juna da aikata laifuka
daban-daban.
Gwamnan jihar Kaduna da ke Najeriya, Nasir El-
Rufai ya yi zargin cewa tsohon mataimakin
shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar yana yin
zagon-kasa ga gwamnatin Shugaba Muhammadu
Buhari.
El-Rufai na yin raddi ne ga zargin da Atiku ya yi
cewa shi butulu ne, kuma ya saba wa ka'idojin
aikin gwamnati a lokacin da yake rike da
mukamai a gwamnatin Olusegun Obasanjo.
A wata hira da Premium Times ta wallafa, Atiku
ya ce shi ya shigar da El-Rufai gwamnati har ya
zama minista, amma da shi "aka yi amfani wurin
zargina da cin hanci", abin da kotu ta wanke ni
daga baya.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, gwamnan El-
Rufai ya yi zargin cewa cin hanci da rashawa
sun dabaibaye Atiku, abin da ya sa yake tsoron
zuwa Amurka.
'An ja zare'
Amma a wata hira da ya yi da BBC, Dr Abubakar
Kari na Jami'ar Abuja, ya ce rikicin da ke
tsakanin mutanen biyu tamkar share fage ne ga
harkokin siyasar shekarar 2019.
A cewarsa, "An fara gwagwarmaya ce ta takarar
shugabanci a zaben shekarar 2019. Ana rade-
radin cewa El-Rufai da Atiku dukkan su suna
sha'awar yin takara.
Abin da wannan hayaniya tasu ta nuna shi ne
kowannen su yana neman gindin-zama ne."
Ya kara da cewa duk da yake Shugaba
Muhammadu Buhari bai taba cewa ba zai tsaya
takara a 2019 ba, wasu na ganin ya tsufa don
haka zai iya ja da baya domin wasu su karba.
Kuma aganinsa hakan ne ya sa El-Rufai da Atiku
ke son nuna wa duniya cewa a shirye suke su
maye gurbin Shugaba Buhari.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "Zaben 2019: 'Atiku da El-Rufai na sha'awar takara'"

Post a Comment