BH: Ina da ja kan yawan mutanen da suka mutu — Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce,
ko kadan ba dai-dai ba ne ace mutanen da suka
mutu a shiyyar Arewa maso gabashin kasar
sakamakon ayyukan Boko Haram, daga shekarar
2009 kawo lokacin da aka bayar da kididdigar,
dubu 10 ne.
A watan maris din da ya gabata ne dai shugaba
Muhammadu Buhari, ya ce 'yan kasar kimanin
dubu 10 ne suka rasu sakamakon rikicin na 'yan
kungiyar Boko Haram, tun daga shekara ta 2009.
Gwamna Kashim Shettima, wanda ya bayyana
hakan ga manema labarai a birnin Abuja, ya
kuma ce an yi hasarar kadarori a yankin na
kusan dala biliyan tara.
"A jihar Borno kadai an kona azuzuwa dubu
5335, an kona makarantun sakandare guda 38
sannan gidajen mutane dubu 956,453 aka kona."
In ji Shettima.
Sai dai kuma gwamnan ya ce, yanzu ba lokacin
ja-in-ja ba ne kan adadin mutanen da suka mutu.
Ya kara da cewa abin da ya kamata a mayar da
hankali a kai, shi ne, yadda za a tallafawa
mutanen da rikicin ya dai-daita.
Kashim Shettima ya kuma bayyana irin karfin
gwaiwar da yake da shi wajen samun tallafin
musamman a karkashin jagorancin shugaba
Muhammadu Buhari.
Sharhi, Usman Minjibir
Kusan za a iya cewa har kawo yanzu babu wata
kididdiga da wani zai iya bugar kirji ya ce ita ce
sahihiya kan adadin mutanen da suka mutu
sanadiyyar rikicin Boko Haram.
Ko da Kungiyoyin Kare Hakkin Bil'adama sun sha
samun karo wajen fitar da alkaluma tsakaninsu
da bangarorin gwamnati musamman ma jami'an
tsaro.
A shekarar 2014, sai da Kungiyar Kare Hakkin
Bil'adama ta Amnesty International ta yi zargin
cewa an kashe mutane sau fiye da biyar din
kididdigar da gwamnatin shugaba Goodluck
Jonathan ta bayar a shekarar.
A lokacin dai gwamnatin shugaba Jonathan ta ce
mutane fiye da dubu 11 ne suka mutu tun daga
2009 lokacin da hare-haren kungiyar ya fara
ta'azzara.
Sai dai kuma mafi yawancin lokaci, a kan kasa
tantance mutanen da 'ya'yan kungiyar Boko
Haram suka kashe da kuma wadanda ake zargin
jami'an tsaron kasar da kisa.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "BH: Ina da ja kan yawan mutanen da suka mutu — Shettima"

Post a Comment