ABOTA DA MUTANAN KIRKI

ABOTA DA MUTANAN KIRKI Annabi s.a.w yana
cewa: (kada kayi abuta da kowa sai
Mumini,kuma kaciyar da abincinka sai ga mai jin
tsoran Allah). @ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ 7341 -Aboki
mumini shine wanda yake kama hannuka zuwa
Wajan Dha'a ga Allah,kuma yake nisantar da kai
daga Sabon Allah, kuma yake ci gaba da yi maka
addua bayan Mutuwar ka,kuma yake cetan ka
awajan Allah a gobe alqiyama. Allah yana cewa:
:" ﺍﻷﺧﻼﺀ ﻳﻮﻣﺌﺬ ﺑﻌﻀﻬﻢ ﻟﺒﻌﺾ ﻋﺪﻭ ﺇﻻ ﺍﻟﻤﺘﻘﻴﻦ : ‏( "(67
ﺍﻟﺰﺧﺮﻑ Ma'ana: "Masõya a yinin nan, sãshensu
zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ
kam mãsu son jũna ne). -Shine wanda yake
kokarin gyara maka munanan Halayanka kuma ya
riqa kokarin baka karfin gwaiwa akan kyawawan
Halinaka. -Shine wanda kuke son junanku saboda
Allah,kuma kuke haduwa da rabuwa saboda da
Allah. -Shine wanda yake karfafa maka gwaiwa
wajan biyayya ga mahaifanka,kuma yake baka
shawara mai amfani game da iyalinka.
******************************* Amma abokin
banza shine: -Wanda yake janka ko kama
hannunka zuwa Wajan sabon Allah. -Kuma yake
nisantar da kai wajan Yawaita Dha'a ga Allah da
bin Umarninsa. -Wanda zai zama abokin adawa
mai tsanani a tsakanin ka da shi a ranar
alqiyama. Allah ka rabamu da abokan banza ka
sanya mu muzama masu abokai mutanan kirki.

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "ABOTA DA MUTANAN KIRKI"

Post a Comment