Ya'yan Trump - Su waye sababbin iyali na farko a Amurka?
Matar Donald Trump da sauran iyalansa sun halarci jawabin nasarsa da ya yi a babban dakin taro na wani Otel da ke birnin New York. To ko Su waye sababbin iyali na farko a Amurka?
1. Barron Trump: Shi kadai ne yaron da Donald ya haifa a aurensa na baya bayan nan da Melina. Duk da cewa ya bayyana a jama'a a lokacin yakin neman zabe, dan shekara 10 din, bai cika bayyana a gaban jama'a ba. Yana wasan golf da mahaifinsa kuma rahotanni sun ce ya iya yaren kasar Slovenia wanda shi ne yaren mahaifiyarsa.
2. Melania Trump:Tsohuwar mai tallan kaya ce kuma haifaffiyar kasar Slovenia ce, ta auri Donald Trump a Janairun shekarar 2005. Ta goyi bayan mijinta a lokacin da wani faifan bidiyo ya bayyana, inda ya nuna shi yana son yin lalata da mata. A shekarar 2016 ne ta jawo ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai bayan da ta yi wani jawabi a babban taron jam'yyar Republican, wanda aka yi zargin ta kwafo ne daga wani jawabi da Michelle Obama, matar Obama ta yi a shekarar 2008.
3. Jared Kushner: Shi ne mijin Ivanka, babbar 'yar Donald. Dan wani hamshakin mai hada-hadar gidaje ne a birnin New York kuma shi ne mai kamfanin jaridar Observer da ke birnin a shekara goma da suka wuce. Rahotanni na cewa Mista Kushner, wanda Bayahude ne, ya bata wa danginsa rai a lokacind a ya yi wani rubutu domin ya kare Donald Trump a kan amfani da ya yi da alamar Star of David a shafinsa na Twitter inda ya soki Hillary Clinton.
4. Ivanka Trump: Ita ce watakila wacce aka fi sani a cikin yaran Donald Trump; ita kadai ce 'yar da ya haifa a aurensu da Ivana matarsa ta farko. Mai tallan tufafi ce a shekarun farko amma a yanzu ita ce mataimakiyar kamfanin Trump kuma alkali ce a wani shirin talabijin da aka yi wa lakabi da The Apprentice. Ta sauya addini ta zama Bayahudiya bayan ta auri Jared a shekarar 2009.
5. Tiffany Trump:Ita ce 'yar da Trump ya haifa a aurensa na biyu da Marla Maples tsohuwar tauraruwa kuma ma'aikiciyar talabijin. Tana son amfani da shafukan sada zumunta musamman Twitter da Instagram, inda take wallafa abubuwan da ke nuna rayuwar jin dadi.
6. Vanessa Trump, nee Haydon, ta auri Donald Trump karami a watan Nuwambar 2005. Ma'auratan na da kananan yara biyar - ciki har da Kai mai shekara takwas. Vanessa ta fara tallan kayan sakawa a lokacin da take yarinya kuma a baya Leonard Dicaprio saurayinta ne.
7. Kai Trump: Ita ce 'yar fari a yara biyar da Vanessa da Donald karami suka haifa.
8. Donald Trump Jr: shi ne babban dan Donald Trump a aurensa na farko da Ivana. A matsayinsa na mataimaki na daya a kamfanin Trump, ya auri Vanessa Haydon bayan mahaifinsa ya gabatar da ita a gare shi a wurin bikin baje-kolin tufafi. Ci gaban da ya samu yana ta jawo masa ce-ce-ku-ce.
9. Eric Trump:Shi ne ɗa na uku a auren Mista Trump da Ivana. Kamar dai sauran 'yan uwansa, shi ma mataimaki ne a kamfanin Trump. Shi ne shugaban kamfanin barasar Trump da ke Virginia da wasu kulub din golf dinsa da ke kasashen waje. A shekarar 2006 ne ya bude gidauniyar Eric Trump, wadda ya bayar da dala miliyan 28 ga wani asibitin binciken da ke taimaka wa yara masu fama da cututtukan da ke barazana ga rayuwarsu.
10. Lara Yunaska:Tsohuwar ma'aikaciyar gidan talabijin ce kuma mace ce mai matukar son hawa doki, ta auri Eric ne a shekarar 2014. Ta karye a hannu makonni biyu kafin aurensu inda Jared Kushner ya kasance waliyi, bayan ta yi sukuwa a kan doki. Ma'auratan ba su da yara, amma suna da kare.

0 Response to "Ya'yan Trump - Su waye sababbin iyali na farko a Amurka?"
Post a Comment