An bayyana alkalan gasar cin kofin Afirka ta Mata

An bayyana sunayen alkalan wasa 25 da za su
jagoranci gasar cin kofin nahiyar Afirka ta
kwallon kafar mata da za a yi a watan
Nuwamba.
Cikin sunayen da hukumar kwallon kafa ta Afirka,
Caf, ta fitar guda 11 ne za su yi hura a
wasannin, yayin da 14 za su taimaka musu
wajen gabatar da aikin.
Za a fara gasar ne a ranar 19 ga watan
Nuwamba zuwa 3 ga watan Disambar 2016 a
birnin Yaounde da Limbe a Kamaru.
Rukunin farko ya kunshi mai masaukin baki
Kamaru da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da
Masar.
Rukuni na biyu ya hada da mai rike da kofin,
Nigeria da Ghana da Kenya da kuma Mali.
Ga jerin alkalan wasan da za su jagoranci
wasannin:
Alkalan wasa
1. Maria Packuita Cynquela Rivet Mauritius
2. Salma Mukansanga Rwanda
3. Gladys Lengwe Zambia
4. Lidya Tafesse Habasha
5. Akhona Zennith Makalima Afirka ta Kudu
6. Jeanne Ekoumou Kamaru
7. Aissata Ameyo Amegee Togo
8. Suavis Iratunga Burundi
9. Caralyne Wanjala Kenya
10. Jonesia Rukyaa Kabakama Tanzaniya
Mai jiran Kar-ta-kwana
11. Letticia Antonella Viana

SUBSCRIBE TO OUR NEWSLETTER

0 Response to "An bayyana alkalan gasar cin kofin Afirka ta Mata"

Post a Comment